Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Larabawa Sun Ce Sam ba Su Yarda A Kai Hari Kan Iraqi ba - 2002-09-05


Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun yi gargadin cewa duk wani harin sojan da Amurka zata kai a kan Iraqi, zai haddasa abinda suka kira "Tsokano tsuliyar Dodo" ne a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministoci daga kasashe 22 na Larabawa sun kammala taron kwanaki biyu a birnin al-Qahira, inda suka ce dukkansu suna yin adawa da duk wani matakin kai farmaki a kan kasar Iraqi.

Ministocin sun fada a cikin sanarwar da suka bayar cewa duk wata barazana nunin karfin da za a yi ma wata kasar Larabawa, ciki har da Iraqi, barazana ce ake yi ga tsaron dukkan kasashen Larabawa.

Babban sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa, Amr Moussa, ya shaidawa 'yan jarida cewar babu wata kasar Larabawa da zata taimaka wa Amurka idan har ta kai farmakin soja a kan Iraqi.

Har ila yau kuma, yayi kira ga hukumomin Iraqi ad su kyale sufetocin makamai na Majalisar Dinkin Duniya su koma cikin kasar domin farautar makaman kare dangi da aka haramtawa kasar mallaka. Ya ce wannan zai nuna cewa ko Iraqi tana da makaman da aka haramta mata mallaka ko kuma a'a.

Kudurorin da ministocin suka cimma a wannan taro nasu, sun kuma yi kiran da a dage takunkumin da aka sanyawa Iraqi a bayan da ta kai harin mamaye Kuwait a shekarar 1990.

XS
SM
MD
LG