Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Singapore ta Damke Mutane 21 Da Ake Zaton 'Yan Ta'adda Ne, Yayin Da Aka Kama Mutum Na Shida A Nan Amurka... - 2002-09-16


Singapore ta ce ta kama mutane 21 da take jin cewa 'yan ta'adda ne a cikin watan da ya shige, akasarinsu 'ya'yan wata kungiyar Musulmi ta yankin da aka ce tana da alaka da kungiyar al-Qa'ida.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta bayar ta ce dukkan mutanen 'yan kasar Singapore ne, kuma 19 daga cikinsu 'ya'yan kungiyar nan ce ta "Jemaah Islamiyya."

An kama 'ya'yan kungiyar fiye da 12 cikin watan Disamba, bisa zargin cewa suna kulla makarkashiyar kai hare-hare kan cibiyoyi da muradun Amurka a Singapore.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan ta ce kama wadannan mutane da aka yi, ya gurgunta kungiyar ta Jemaah Islamiyya a Singapore.

A nan Amurka kuma, hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya ta kama mutum na shida na wata tungar da ake kyautata zaton makwancin 'yan ta'adda ne a yankin birnin Buffalo dake Jihar New York.

Jami'an Amurka sun ce kwanakin nan aka kama Mukhtar al-Bakry a kasar Bahrain, a lokacin da yake shirye-shiryen aurensa a kasar. Nan gaba a yau ake sa ran za a bada cikakkiyar sanarwa game da kama shi.

Mutane biyar din da ake zargin cewa abokan hada bakinsa ne, sun bayyana ranar asabar a gaban wata kotu a birnin buffalo, inda aka tuhume su da laifin bayar da agaji ga 'yan ta'addar al-Qa'ida.

Dukkansu Amurkawa ne 'yan tsatson Yemen.

A wani labarin kuma, Pakistan ta nuna alamun cewar zata mikawa Amurka wani jigon kungiyar al-Qa'ida, Ramzi Binalshibh, wanda aka kama ranar laraba a birnin Karachi.

XS
SM
MD
LG