Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawar Zimbabwe Sun Yi Zargin Cewa An Gana Musu Azaba - 2002-09-30


Wasu 'yan jam'iyyar adawar kasar Zimbabwe su biyar sun ce an gana musu azaba a lokacin da suke hannun 'yan sanda.

A ranar alhamis da ta shige 'yan sanda suka kama wadannan matasa su biyar daga jam'iyyar "MDC" bisa zargin tayar da hankalin jama'a.

An yi kame-kame irin wannan da dama kafin, da kuma a lokacin zabubbukan da aka gudanar a ranakun asabar da lahadi, inda gwamnati da 'yan adawa suka yi ta zargin juna da laifin haddasa wannan fitina.

'Yan adawar su biyar sun bayyana a gaban kotu yau litinin, an kuma bada belinsu. Ta bakin lauyoyinsu, mutanen biyar sun ce an yi ta cin zarafi tare da gana musu azaba.

Babu 'yan kallo masu zaman kansu da suka sanya idanu kan zabubbukan da aka yi na kansiloli.

XS
SM
MD
LG