Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Birnin Washington D.C. Da Kewaye Suna Zaune Cikin Fargaba... - 2002-10-07


A bayan kashe-kashen da wani dan bindiga yayi a makon jiya a nan ciki da kuma kewayen birnin Washington D.C., wani harbin na dabam da aka yi da nufin kisa a wata makaranta ta sanya cikin mutane ya dura ruwa.

'Yan sandan Jihar Maryland da hukumomin tarayya a nan Amurka suna binciken harbe wani yaro dan shekara 13 da aka yi a kofar makarantarsu a garin Bowie na Jihar Maryland, domin su ga ko yana da alaka da harbe-harben da wani ko wasu 'yan bindiga suka yi makon jiya inda aka kashe mutane 6 a ciki da kuma kewayen nan birnin Washington.

An harbi wannan yaro a kirji a daidai lokacin da ya isa makaranta. A yanzu haka, yana babban asibitin yara na kasa a nan Washington inda aka yi masa tiyata, kuma an ce yana kwance rai hannun Allah.

'Yan sanda suka ce an yi amfani da harsasai masu barna samfurin irin na soja wajen kashe akalla mutane hudu daga cikin 6 na makon jiya.

Dukkan wadanda aka harba din, an harbe su ne sau daya tak daga nesa da bindiga mai karfin gaske irinta farauta, kuma da alamun babu wani daga cikinsu da ya san mutumin dake yin harbe-harben.

XS
SM
MD
LG