Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yajin Aiki A Kasar Venezuela... - 2002-10-21


An rufe dubban kantuna da ofisoshi da makarantu na tsawon sa'o'i 12 a kasar Venezuela a wani yajin aikin da aka shirya da nufin neman shugaba Hugo Chavez da yayi murabus ko kuma dai ya sa a gudanar da sabon zabe.

Dogarawan tsaron kasa suna sintiri a titunan Caracas, babban birnin kasar, domin tabbatar da tsaro, a bayan da magoya bayan shugaba Chavez suka yi barazanar kwasar ganima a kantunan da aka rufe.

Kungiyar ma'aikata ta kasar Venezuela da kungiyar 'yan kasuwa da ake kira "Fedecamaras" sun bayyana cewa an samu nasarar wannan yajin aiki, inda suka ce kashi 75 daga cikin 100 na membobinsu sun yi aiki da wannan umurni.

Amma kuma kamfanin mai na kasar, "Petroleos de Venezuela", ya ce ayyukanssa sun gudana kamar yadda aka saba, duk da cewa wasu daga cikin ma'aikata sun yi zamansu a gida.

XS
SM
MD
LG