Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Suna Yin Garkuwa Da Mutane 700 Cikin Dakin Sinima A Rasha - 2002-10-23


An bada rahoton cewa wasu 'yan bindiga da suka kama mutane suna yin garkuwa da su cikin wani dakin sinima a birnin Moscow, suna dasa bama-bamai a cikin wannan wuri.

Gidan telebijin na Rasha ya ce har yanzu wadannan 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, ba su bayyanawa hukumomin Rasha bukatunsu ba.

Zaratan sojojin Rasha sun yi tsinkewa dakin sinimar dake wata unguwar ma'aikata a bangaren kudu maso gabashin birnin Moscow.

'Yan bindiga su kimanin 20 sun abka cikin dakin sinimar cikin daren nan na laraba, suka kama mutane kimanin 700 suna yin garkuwa da su. Rahotanni sun ce 'yan bindigar suna sako yara kanana daga cikin wadanda ke dakin sinimar.

XS
SM
MD
LG