Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhammad Ali Yana Ziyarar Kasar Afghanistan - 2002-11-17


Mashahurin zakaran damben duniya mai ritaya, Muhammad Ali, yana kasar Afghanistan domin janyo hankalin duniya ga bukatun sake gina kasar da yaki ya lalata.

Yau lahadi Muhammad Ali mai shekaru 60 da haihuwa ya isa birnin Kabul, inda zai gana da shugaba Hamid Karzai, tare da ziyartar matasa 'yan wasa a wani kulob na wasannin motsa jiki.

Muhammad Ali, wanda zai rike matsayin jakadan Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, lokacin wannan ziyarar kwanaki uku, zai ziyarci wata makarantar yara mata, da kuma wani gidan burodi na mata.

Kakakin MDD, Manoel de Almeida e Silva, ya ce Muhammad Ali ya shafe shekara da shekaru yana tallafawa ayyukan jinkai, kuma ya nuna sha'awa ta musamman ta kula da jin dadin yara da marasa galihu.

Muhammad Ali yayi farin jini sosai a kasar Afghanistan lokacin da ya zamo Musulmi a shekarar 1964, watau shekarar da ya fara zama zakaran damben duniya.

XS
SM
MD
LG