Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Tana Shirin Cilla Dan Sama Jannatinta Zuwa Samaniya - 2003-01-02


China ta ce nan gaba cikin wannan shekara zata harba dan sama jannatinta na farko.

Kafofin yada labaran China sun ambaci wani babban jami'in hukumar binciken sararin samaniya ta kasar yana mai fadin cewa kumbonsu mai suna "Shenzou-Five" zai tashi zuwa samaniya dauke da dan sama jannati a cikin watanni shida na karshen wannan sabuwar shekara.

Idan har ta samu nasara, China zata bi sahun Amurka da Rasha a zaman kasashen da suka cilla 'yan sama jannati zuwa samaniya. 'Yan sama jannatin wasu kasashen da dama sun tafi samaniya, amma a cikin kumbunan Amurka da Rasha.

A halin da ake ciki dai, wani kumbon da China ta harba yana ci gaba da zagaya duniya kowace sa'a daya da rabi. A ranar litinin aka cilla wannan kumbo mai suna "Shenzhou-Four" daga hamadar Gobi. Ana sa ran kumbon zai ci gaba da zaga duniya na tsawon kwanaki uku ko hudu masu zuwa.

XS
SM
MD
LG