Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colin Powell Zai Gabatarwa Da Majalisar Dinkin Duniya 'Kwakkwarar' Shaida - 2003-02-05


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce a yau laraba zai gabatarwa da Majalisar Dinkin Duniya "Kwakkwarar Shaidar" cewa Iraqi tana boye makaman kare-dangin da aka haramta mata mallaka.

Jami'ai suka ce Mr. Powell zai gabatar da hotunan leken asiri da kuma muryoyin jami'an gwamnatin Iraqi da aka yi satar dauka suna tattauna yadda zasu boye haramtattun makamai.

Iraqi ta ce tana bada cikakken hadin kai ga sufetocin MDD, kuma ba ta da makaman kare-dangi. Ta ce Mr. Powell zai gabatar da shaidar karya ce kawai wadda Amurka ta kitsa.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa, wadda kasarsa ke shugabancin Kwamitin Sulhun MDD a yanzu, ya ce sufetocin makamai suna bukatar karin lokaci domin su gudanar da ayyukansu.

Sai dai sakataren harkokin wajen Britaniya, Jack Straw, ya rubuta cikin jaridar Times ta London a yau laraba cewa kiran da a karawa sufetocin lokaci, aikin banza ne kawai idan har Saddam Hussein ya ki ba da hadin kai.

XS
SM
MD
LG