Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Gabatarwa Da Kwamitin Sulhu Shaida... - 2003-02-06


A jiya laraba sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya gabatarwa da Kwamitin sulhun MDD shaidar da a cewar gwamnatin shugaba Bush ta nuna cewa Iraqi tana yaudarar sufetocin makamai na majalisar, yayin da take ci gaba da kera makaman kare dangi. Wakiliyar Muryar Amurka a New York, Barbara Schoetzau, ta ce Mr. Powell ya kuma gabatar da shaidar da ya ce ta nuna hulda a tsakanin hukumomin Iraqi da kungiyar 'yan ta'adda ta al-Qa'ida.

Mr. Powell yayi amfani da wasu hotunan da aka dauka daga tauraron dan adam, da kuma muryoyin da aka yi satar dauka ta wayoyin tarho domin jaddada hujjar Amurka ta raba Iraqi da makamanta, koda da karfin tuwo ne. Yayi ta nanata cewar Iraqi tana yaudarar sufetocin makamai tare da sanya dakunan binciken kimiyyarta na makamai masu guba cikin motocin tafi da gidanka.

Sakataren harkokin wajen ya nuna hotunan da aka dauka daga sama wadanda a cewarsa wurare ne na kera makamai masu guba. Ya kuma nuna hotunan wadannan wurare a bayan da aka share su kaf. Ya sanya kaset dauke da muryoyin hafsoshin sojan Iraqi wadanda ya ce suna magana ne kan yadda za a boye makamai. Mr. Powell ya ce MDD tana fuskantar kasadar zamowa maras tasiri idan har ta kyale Iraqi ta ci gaba da yin ko oho da kudurorin Kwamitin sulhu.
ACT: POWELL: "The issue before us is not how much time we are willing to give the inspectors to be....."

FASSARA: Batun dake gabanmu ba shine na yawan karin lokacin da zamu bai wa sufetoci domin Iraqi ta ci gaba da yaudararsu ba, batun shine har yaushe zamu zauna muna kallon Iraqi tana kin aiki da kudurorin nan, kafin mu tashi mu ce ya isa haka? KARSHEN FASSARA

CI GABA: Mr. Powell ya shaidawa wakilan Kwamitin Sulhu cewar Iraqi tana da abubuwa biyu daga cikin uku da ake bukata domin kera bam na nukiliya, watau kwararrun masana kimiyya da kuma zanen yadda zata kera bam din. Mr. Powell ya ce Saddam Hussein ya kuduri aniyar samun abu na ukun, watau tataccen karfen Uranium.

A karon farko kuma Mr. Powell ya bayyana shaidar da Amurka ta ce tana da ita wadda ta nuna hulda tsakanin Iraqi ad kungiyar al-Qa'ida. A cewarsa, Iraqi tana bada mafaka ga "wata mummunar kungiyar ta'addanci dake karkashin Abu Musab Zarqawi, wani abokin Osama bin Laden." A cewar Mr. Powell, yau watanni takwas ke nan 'ya'yan wannan kungiya suna watayawarsu a cikin Bagadaza. A karshe dai, Mr. Powell ya gargadi MDD cewar kada ta dauka cewa Saddam Hussein ba zai yi amfani da makaman da yake kerawa ba.
ACT: POWELL: "The United States will not and cannot run that risk to the American people. Leaving Saddam..."

FASSARA: Amurka ba zata iya kyale Amurkawa su fuskanci irin wannan hadarin ba. Kyale Saddam Hussein dauke da makaman kare dangi na watanni ko shekaru ba zabi ba ne a garemu, musamman a bayan abinda ya faru ranar 11 ga watan satumbar 2001. KARSHEN FASSARA

CI GABA: Mr. Powell yayi kira ga wakilan Kwamitin Sulhun da kada su kasa fuskantar kalubalen dake gabansu.

XS
SM
MD
LG