Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allurar Rigakafin Cutar Kanjamau Ta AIDS Tana Iya Kare Wasu Jinsuna - 2003-02-24


Wata sabuwar allurar rigakafin cutar kanajamau ta AIDS ta gwaji ta nuna alamun kare bakaken fata da Asiyawa, amma kuma babu alamar cewa zata kare sauran jama'a daga wannan mummunar cuta.

Jami'an kamfanin VaxGen dake Jihar California, sun ce sakamakon da aka samu na gwajin da aka yi da wannan allura mai suna AIDSVAX ya nuna cewa kamuwa da wannan cuta ta ragu ne kawai a kashi 4 daga cikin 100 na mutane dubu 5 da 400 da aka yi musu allurar.

Amma kuma daga cikinsu, kashi 67 daga cikin 100 na bakaken fata da Asiyawa sun samu raguwar kamuwa da cutar idan an kwatanta da wadanda aka yi musu wata allurar da babu maganin ciki.

Kamfanin VaxGen ya ce wannan shine karon farko da aka tabbatar da cewa wata allura tayi rigakafin kamuwa da kwayar halittar cuta ta HIV mai haddasa cutar AIDS. Masu bincike suka ce yi nazari sosai su ga ko me ya sa allurar ta fi yin aiki ma wasu jinsuna fiye da wasu.

Cutar AIDS ta kashe mutane fiye da miliyan 20 a fadin duniya, yayin da wasu miliyan 40 suke dauke da kwayar cutar a yanzu haka.

XS
SM
MD
LG