Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Britaniya Zasu Gabatar Da Sabon Kuduri Kan Iraqi Yau Litinin A MDD - 2003-02-24


Amurka da Britaniya zasu gabatarwa da Kwamitin Sulhun MDD wani sabon kuduri kan kasar Iraqi nan gaba a yau litinin.

Ana sa ran cewa wannan kuduri zai ce shugaba Saddam Hussein na Iraqi yayi watsi da damar karshe da aka ba shi ta kwance damarar yaki cikin lumana.

Wani bangare na wannan sabon kudurin da aka samu gani ya ce Iraqi zata fuskanci martani mai tsanani idan har ba ta yi aiki da umurnin MDD na ta kwance damara ba.

Kakakin fadar White House, Ari Fleischer, ya ce kalmomin dake kunshe cikin kudurin ba yawa, kuma ba tare da kauce-kauce ba zasu bayyana muhimmancin kuduri na 1441 na Kwamitin Sulhun MDD. Ya ce kudurin ba zai tsayar da lokaci na jefa kuri'a ba, amma ya bayyana a fili cewa shugaba Bush yana sa ran wakilan kwamitin zasu nazarci kudurin ba tare da dogon turanci ba.

Kwamitin Sulhun ya bada sanarwar cewa a daidai wannan lokaci ne, watau da karfe 9.30 na dare agogon Nijeriya, yake gudanar da taro a asirce.

Kafin a zartas da wannan kuduri, sai ya samu kuri'u 9 a Kwamitin Sulhun, sai kuma idan Faransa ko Rasha ko china ba ta hau kujerar-na-ki ba. A yanzu dai kuri'u 4 kawai Amurka take da shi cikin Kwamitin Sulhun, yayin da sauran 11 suke da ra'ayin ci gaba da ayyukan binciken makamai.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa, ya bada sanarwar gabatar da wani sabon kudurin hadin guiwa na Faransa da Jamus da Rasha na kwance damarar yakin Iraqi daki-daki ba tare da gwabza yaki ba.

XS
SM
MD
LG