Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 15 Sun Mutu A Isra'ila - 2003-03-05


Jami'an Isra'ila sun ce mutane akalla 15 sun mutu yayin da wasu mutanen har 30 suka ji rauni a bayan da wani abu ya fashe cikin wata motar safa yau laraba da tsakar rana a birnin Haifa dake arewacin Isra'ila.

Motocin daukar marasa lafiya sun garzaya zuwa wurin da wannan lamari ya faru, yayin da ake fadin cewa da yawa daga cikin wadanda suka ji raunin suna cikin hali mai tsananin gaske.

'Yan sandan Isra'ila sun ce wannan harin ta'addanci ne, amma kuma babu wanda ya dauki alhakin kai shi.

Wannan lamari na yau ya biyo bayan kama Falasdinawa su akalla 20 da sojojin Isra’ila suka yi cikin dare, tare da rushe gidan wani dan kishin Falasdinu a yankin yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG