Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Tilas Duniya Ta Takali Iraqi - 2003-03-07


Shugaba Bush ya ce lokaci yayi da duniya zata takali Iraqi game da muggan makamanta na kare-dangi.

A lokacin da yake hira da 'yan jarida a daren alhamis, shugaban na Amurka ya ce tilas duniya ta fuskanci yiwuwar daukar matakan soja a bayan da aka shafe shekaru 12 ana kokarin diflomasiyya domin ganin cewa shugaba Saddam Hussein ya lalata makamansa na kare-dangi.

A yayin da ake sauran kwanaki kadan Kwamitin Sulhun MDD ya jefa kuri'a kan kudurin da zai ba da iznin yaki, a bayan rahoton da sufetocin makamai zasu gabatar in an jima, Mr. Bush ya ce hanyar sulhu ta kasa yin aiki a Iraqi, kuma shi a shirye yake yayi amfani da karfi, koda Kwamitin sulhun bai amince da kudurin ba.

ACT: BUSH: "If we need to act, we will act, and we really don't need United Nations approval to do so."

FASSARA: Idan akwai bukatar daukar mataki (na soja), to zamu dauka, (domin) a gaskiya ma ba mu bukatar amincewar MDD kafin mu yi haka.

Shugaban ya ce har yanzu bai yanke shawarar kai farmakin soja ba, amma kuma ya ce idan yayi haka, to sojojin Amurka zasu kawar da saddam Hussein daga kan mulki su kafa abinda ya kira kasa mai adalci da zata wakilci dukkan al'ummar Iraqi.

Shugaban yayi watsi da masu neman bai wa Iraqi karin lokaci na yin aiki da kudurorin binciken makamai, yana mai fadin cewa idan har da gaske Saddam Hussein yana da niyyar kwance damarar yaki, ai da tuni yayi.

ACT: BUSH: "Inspection teams do not need more time or more personnel. All they need is what thwey have never received: the full cooperation of the Iraqi..."

FASSARA: Kungiyoyin bincike ba su bukatar karin lokaci ko karin sufetoci. Abinda kawai suke bukata shine abinda tun farko aka hana su, watau cikakken hadin kai daga gwamnatin Iraqi. Ba zamu amince da hadin kai cikin cokalin da ake ba su ba.

Mr. Bush ya ce abu daya tak da suke bukata shine Iraqi ta lalata muggan makamanta baki daya. Ya ce idan ba haka ba kuwa, to Iraqi barazana ce ga Amurka da kawayenta a saboda zata iya taimakawa 'yan ta'adda wajen yin aiki da makaman kare-dangi.

ACT: BUSH: "The risk of doing nothing, the risk of hoping that Saddam Hussein changes his mind and becomes a gentle soul, the risk that somehow inaction..."

FASSARA: Hatsarin dake tattare da kasa yin wani abu, da hatsarin dake tattare da tunanin cewa Saddam Hussein zai sauya halinsa ya zamo mutum na gari, kasada ce da ba zan iya dauka ba wajen kare rayukan Amurkawa.

Faransa dai ta ce babu abinda kai hari kan Iraqi zai haddasa im ban da kara yawan hare-haren ta'addanci.

XS
SM
MD
LG