Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Bin Diddigin Gaskiya Da Sasanta Al'ummar Afirka Ta Kudu Ta Mika Rahoton Da Aka Jima Ana Sa Rai - 2003-03-21


Tsohon shugaban Hukumar bin Diddigin Gaskiya da sasanta Al'ummar Afirka ta Kudu, ya mika kammalallen rahoton kwamitin ga shugaba Thabo Mbeki.

Archbishop Desmond Tutu ya mika sauran kundaye biyu na rahoton Kwamitin yau Jumma'a a wajen wani bukin da aka yi a birnin Pretoria.

A lokacin da yake mika rahoton, Archbishop Tutu yayi rokon da a gaggauta biyan diyya ga mutanen ad suka tagayyara a sanadin mulkin wariyar launin fata ta turawa 'yan tsiraru.

Rahoton ya kunshi shawarwari da dama, ciki har da kafa wani haraji na attajirai da kamfanonin Afirka ta Kudu zasu biya domin taimakawa wajen samun miliyoyin dalolin da ake bukata na biyan diyya ga wadanda mulkin wariya ya lahanta.

An kafa wannan hukuma a shekarar 1995 domin ta binciki keta hakkin bil Adama da sauran laifuffukan da aka aikata a zamanin mulkin turawa 'yan tsiraru na kasar.

Mutane dubu 21 suka gabatar da shaida a gaban hukumar. An yi ahuwa ma wasu dubu 1 da 200 daga cikinsu.

XS
SM
MD
LG