Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Annobar Cutar Kanjamau, AIDS, Zata Gurgunta Kokarin Yaki Da Cutar Tarin Fuka - 2003-03-24


Tarayyar kungiyoyin agajin Red Cross da Red Crescent ta duniya ta ce nan ba da jimawa ba annobar cutar kanjamau ta AIDS, ko SIDA, zata iya warware dukkan ci gaban da aka samu wajen yakar tarin fuka a duniya.

A cikin sanarwar da ta bayar a wannan Rana ta Tarin Fuka a fadin duniya (yau litinin), tarayyar kungiyoyin agajin biyu ta ce a yanzu tarin fuka ya zamo ciwon da ya fi kashe mutanen dake dauke da kwayar halittar cuta ta HIV, mai haddasa kanjamau.

Babban jami'in kula da yaki da tarin fuka na tarayyar, Terhi Heinasmaki, ya ce za a iya shawo kan cutar kanjamau da kuma tarin fuka ne ta hanyar daukar matakan murkushe su a hade. Jami'in ya ce yadda jama'a ke kyamar masu fama da wadannan cututtuka biyu, ya sa masu fama suna zamowa saniyar ware, ko kuma suna rufewa jama'a idan suka kamu da cututtukan.

Kungiyoyin agajin biyu sun ce tun 2000 aka daina samun karuwar masu fama da tarin fuka a duniya, inda aka ce a yanzu akwai mutane kimanin miliyan 3 da dubu 600 dake dauke ad cutar. Amma kuma, yawan karuwar masu fama da cutar kanjamau zata iya azizita yaduwar tarin fuka.

XS
SM
MD
LG