Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Iraqi Sun Yi Tur Da Matsayin Kasashen Larabawa - 2003-03-25


Manyan jami'an Iraqi sun fito a yau talata suna sukar shugabannin sauran kasashen larabawa saboda rashin ba su goyon baya sosai a yakin da suke yi da sojojin taron dangi.

Mataimakin shugaban Iraqi, Taha Yasin Ramadan, ya soki lamirin kasashen larabawa wadanda suka ki daukar matakai na gari game da harin da Amurka da Britaniya ke kai musu. Malam Ramadan yayi kira ga kasashen larabawa da su kori jami'an jakadancin kasashen biyu.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida a Bagadaza, Malam Ramadan ya ce bai ga dalilin da ya sa kasashen suka kasa tsinke kai man fetur zuwa kasashen da ya kira 'yan cin zali ba. Ba tare da ambaton sunan Sa'udiyya ba, mataimakin shugaban na Iraqi ya soki gwamnatin Sa'udiyya da laifin kara yawan man da take hakowa domin cike gurbin wanda aka rasa a saboda yaki.

Har ila yau ya zargi wasu kasashen larabawa da laifin bayar da bayanan asiri ga sojojin taron dangi, abinda ya ba su damar sanin wuraren da suke kaiwa farmaki a cikin Iraqi.

Malam Ramadan ya kuma musanta ikirarin da jami'an Britaniya suka yi cewar garin Umm Qasr mai tashar jiragen ruwa yana hannun sojojin taron dangi.

A halin da ake ciki dai, Shugaba Saddam Hussein na Iraqi ya fito a cikin telebijin, yana yin kira ga sojojinsa da su kare kasarsu, yayin da jami'an Iraqi suka ce zasu tura karin kayayyakin bukatu da na fada zuwa kudancin Iraqi domin jama'a su samu damar kare kasarsu.

Gidan telebijin na Iraqi ya nuna hotunan wasu mayakan sama guda biyu na Amurka, wadanda aka harbo jirgin samansu na kai farmaki na helkwafta ranar litinin a wajen birnin Bagadaza. Kwamandan sojojin taron dangi, Janar Tommy Franks, ya shaidawa 'yan jarida cewar wannan jirgin helkwafta na daya daga cikin na kai farmakin da aka tura cikin Iraqi a ranar litinin, amma ya musanta ikirarin da Iraqi tayi cewar wasu manoma ne suka harbo jirgin.

XS
SM
MD
LG