Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An fara kidaya Kuri'u a Nigeria - 2003-04-13


An fara kidaya kuri'un da aka kada a zaben wakilan majalisun dokokin Nigeriya a jiya asabar.

Wasu 'yan Nigeriya sun Bara cewa an yi latti wajen fara zaben, domin ba a bude tashoshin zaben ba a wasu yankunan sai bayan Sa'oi masu yawa.

To amma jami'an hukumar zaben kasar ta Nigeriya-- INEC, sun ce sun kashe duk tsawon daren Juma'a suna rarraba katunan zabe zuwa tashoshi dubu 150

A Abuja, abokin aikiunmu Ibrahim Alfa Ahmed da wakilanmu Babangida Jibrin da Madina Dauda sun ce an yi fama da ruwan sama a birnin. A birnin Ikko kuwa, ko bayan ruwan saman da aka yi, haka kuma an samu jinkirin fara zaben a wasu tashoshin. To amma duk da haka masu lura da harkokin yau da kullum sun ce tunda safe dinbim mutane suka fita domin kada kuri'unsu.

Ana daukar wannan zabe na jiya da kuma na shugaban kasa da gwamnoni da za a yi a ranar 19 ga wannan Wata, na zama wani zakaran-gwajin-dafi ga mulkin demokaradiyyar Nigeriya na shekaru 4, bayan da sojoji suka mika mulki a kasar a shekarar 1999.

Shugaba Obasanjo na daga cikin mutanen da suka fita a jiyan domin kada kuri'unsu. Shugaban wanda yake sake yin takara ya kada kuri'arsa ne a garinsu Abekuta na jihar Ogun.

Duk da yadda aka zaci za a yi fama da yamutsi da tarzoma a wannan zabe, amma a zahiri tarzomar da aka yi a lokacin zaben bata taka kara ta karya ba. Hatta ma a yankin Niger Delta mai arzikin Mai, inda a kwanaki aka yi fama da tashin-tashina, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali kadaran-kadahan.

Shi ma Mohammdu Buhari dan takarar shugabgancin kasa na jam'iyyar ANPP ya kada tasa kuri'ar a garinsu Daura dake jihar Katsina a arewacin kasar. Duk da yake rahotannin sun ce Matarsa bata samu sukunin kada tata kuri'ar ba, domin duk da cewa ta fita ta yi zaben a jiya, amma kuma babu sunanta a littafin masu zabe.

'Yan takara dubu 3 ne suke kokawar darewa kan kujeru 469 na majalisun na tarayya.

XS
SM
MD
LG