Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saddam Hussein Yana Nan Da Rai... - 2003-06-20


Wata jaridar Amurka ta ce a yanzu, jami'an leken asiri sun yi imanin cewa Saddam Hussein ya kubuta daga hare-haren da aka kai masa, kuma magoya bayansu sun boye shi a wani wuri a cikin Iraqi.

A wani rahoton da ya sabawa ikirarin da rundunar soja ta yi a watannin Maris da Afrilu cewa watakila hare-haren bam na Amurka sun kashe Saddam Hussein, jaridar New York Times ta ce a yanzu kwararrun leken asiri na Amurka sun fi kyautata zaton cewa yana da rai.

Jaridar ta ce jami'an leken asirin sun bayyana wannan matsayi nasu ne a saboda bayanan da suka ji daga maganganun magoya bayan Saddam da aka yi satar ji. Jami'an Amurka suka ce wadannan bayanan sirri da aka samu, sun sa an kara kokarin da ake yi na farautar Saddam da 'ya'yansa maza biyu, Uday da Qusay.

A halin da ake ciki, an sake kai hari kan sojojin Amurka a Iraqi, wannan karon a tsohuwar tungar Saddam Hussein ta Fallujah.

An raunata sojojin Amurka 2 jiya alhamis da maraice a lokacin da wasu mutanen da ba a san ko su wanene ba suka harba gurneti kan wata tashar samar da wutar lantarki.

An kashe sojojin Amurka akalla uku a hare-hare cikin makon nan. Jami'an Amurka suna dora laifin hare-haren a kan magoya bayan Saddam Hussein.

XS
SM
MD
LG