Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Charles Taylor Na Liberiya Ya Lashi Takobin Ci Gaba Da Mulki - 2003-06-20


Shugaba Charles Taylor na Liberiya ya ce ba zai sauka ba sai wa'adinsa na mulki ya cika, abinda ya jefa shirin wanzar da zaman lafiya a kasar cikin tababa.

Mr. Taylor ya ce idan wa'adin da aka zabe shi kai ya cika a watan Janairu, zai mika mulki hannun mataimakinsa domin mulkin wucin gadi. Har ila yau ya ce yana da ikon tsayawa takarar shugaban kasa a duk lokacin da aka gudanar da zabe a Liberiya.

Wannan sanarwa ta zo kwanaki uku a bayan da aka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin gwamnatinsa da wasu kungiyoyin 'yan tawaye biyu da suka yi kofar-rago wa Monrovia, babban birnin kasar.

Yarjejeniyar ta yi kiran da nan take a fara tattaunawar kwanaki 30 da nufin kafa gwamnatin rikon kwarya wadda ba zata kunshi Mr. Taylor ba.

Amma kuma yarjejeniyar ba ta kayyade ko wannan gwamnatin rikon kwarya zata fara aiki da zarar an kammala tattaunawar ne ko kuma sai a karshen wa'adin Mr. Taylor a farkon shekara mai zuwa ba.

Har yanzu kungiyoyin 'yan tawayen Liberiya ba su mayar da martani game da wannan furuci na shugaba Taylor ba. Kungiyoyin suna rike da kashi 2 cikin 3 na Liberiya.

XS
SM
MD
LG