Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Shugaba Gnassingbe Eyadema Na Togo - 2003-06-20


Mutumin da ya fi kowa jimawa kan karagar mulki a nahiyar Afirka, Shugaba Gnassingbe Eyadema na Togo, ya sake rantsuwar karbar karin wa'adin shekaru 5 kan wannan kujera.

A yau Jumma'a a birnin Lome aka rantsar da Mr. Eyadema, wanda tun shekarar 1967 yake kan karagar mulki.

Hukumar zabe ta Togo ta ce Mr. Eyadema shine ya lashe zaben ranar 1 ga watan nan na Yuni da kusan kashi 58 daga cikin 100 na yawan kuri'un da aka jefa. Amma kuma 'yan adawa sun ce an tabka magudi.

Babban dan takarar masu adawa, Bob Emmanuel Akitani, wanda yayi ikirarin cewa shine ya lashe wannan zabe, ya ce shi ma zai kafa tasa gwamnatin. Yayi kira ga magoya bayansa da su fara tayar da kayar baya cikin 'yan kwanakin nan dake tafe.

XS
SM
MD
LG