Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Saman Sojan Aljeriya Ya Fadi A Yamma Da Algiers - 2003-06-30


Gidan rediyon Aljeriya ya ce wani jirgin saman soja ya fadi kan wasu gidajen jama'a a yamma da Algiers, babban birnin kasar.

Har yanzu babu cikakken bayani na wannan hatsari. Amma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci wani jami'in soja yana fadin cewa an gano gawarwaki 17, cikinsu har da ma'aikatan wannan jirgi kirar Hercules C-130, su hudu.

Wannan hatsari ya faru kimanin kilomita 40 a yamma da babban birnin kasar, a kusa da filin jirgin saman soja na Boufarik.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters dake wurin, ya ce jirgin ya fada kan wasu gine-gine dake kusa da filin jirgin jim kadan da tashinsa.

XS
SM
MD
LG