Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Rana Ta Hudu Ta Yajin Aikin Gama-Gari A Nijeriya - 2003-07-03


Tattaunawa a tsakanin shugabannin kwadago da gwamnatin Nijeriya ta wargaje, yayin da aka shiga rana ta hudu da fara yajin aiki na kasa baki daya dangane da karin farashin mai.

Rahotanni sun ce har yanzu akwai sabani sosai kan matsayin bangarorin biyu game da karin farashin man a lokacin da aka tsinke tattaunawa yau alhamis da safe. Ana iya komawa kan teburin shawarwari nan gaba a yau din.

'Yan sandan Nijeriya sun yi alkawarin ci gaba da murkushe 'yan zanga-zanga, wadanda suka fara yajin aiki ranar litinin, a bayan da gwamnati ta yi karin fiye da kashi hamsin cikin dari kan farashin mai.

A jiya laraba, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da harsasai na zahiri a kan 'yan zanga-zanga a Abuja, babban birnin kasar, a wani yunkuri na neman tarwatsa su.

Rahotanni sun ce mutane masu yawa sun ji rauni a lokacin da mutane fiye da dubu daya suka ranta da gudu a rude daga babbar kasuwar Abuja. Wasu rahotannin sun ce 'yan sandan suna mayar da martani ne ga rikicin da ake yi a tsakanin 'yan kungiyar kwadago da 'yan kasuwar da suka ki rufe kantunansu.

Babbar kungiyar kwadago ta Nijeriya ta zargi 'yan sanda da daukar matakan keta a kan 'yan zanga-zanga.

XS
SM
MD
LG