Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Soja Sun bayar Da Sanarwar Rushe Gwamnatin Sao Tome - 2003-07-16


Bijirarrun sojoji a tarayyar tsibiran Sao Tome da Principe sun kifar da gwamnati a wani juyin mulkin da babu zub da jini.

A cikin sakon da gidan rediyon kasar ya watsa, wani mutumin da ba a bayyan ako wanene ba ya ce shugabannin juyin mulkin sun rushe dukkan hukumomin gwamnati, sun kuma kafa gwamnatin mulkin soja.

Sanarwar ta ce an yi juyin mulkin ne a saboda sukurkucewar harkokin siyasa, da tattalin arziki da kuma halin rayuwar al'umma cikin 'yan kwanakin nan a tsibiran na Sao Tome da Principe.

Tun fari a yau laraba, an ji kararrakin harbe-harben bindigogi da fashe-fashen gurneti a cikin Sao Tome, babban birnin kasar, yayin da daruruwan sojoji suka kama manyan jami'an gwamnati tare da muhimman gine-gine. Ba a samun rahoton mutuwa ko jin rauni ba.

Sojoji suna yin sintiri a titunan babban birnin kasar.

Tun da fari, an kama firayim minista mace ta farko a tarihin kasar, Maria das Neves, da ministan man fetur Joaquim Rafael Branco, aka tsare su.

An yi imanin cewa Manjo Fernando Pereira shine madugun 'yan juyin mulkin, wanda aka yi a lokacin da shugaba Fradique de Menezes yake ziyarar radin kansa a Nijeriya. kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci shugaban yana rokon dukkan masu kwadayin dimokuradiyya, da shugabannin Afirka da na sauran kasashen duniya da su mayar da shi kan karagar mulkinsa.

Wannan 'yar mitsitsin kasa dai tana da mutane kimanin dubu 150 ne kawai. Tana daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya, amma kuma dimbin arzikin man fetur da aka gano, da irin ganimar da ake ganin kasar zata kwasa, ya haddasa zaman doya da manja a tsakanin al'ummar wannan kasa.

XS
SM
MD
LG