Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shawarwari Ga Mai Niyyar Ziyarar Amurka - 2003-07-28


Mutane da yawa sukan taho nan Amurka, ya Allah ko domin ziyarar shakatawa, ko aiki, ko kuma dai ganin 'yan'uwa da abokan arziki ko kasuwanci. Ga wasu bayanai, ko matakan da zasu iya taimakawa mai niyyar zuwa nan Amurka domin gujewa samun matsaloli a kan hanya. Allah Ya bada sa'ar tafiya, Ya kuma kiyaye hanya, amin:

DOMIN TABBATAR DA KARE KANKA, DAUKI WADANNAN MATAKAI:

1. Kada ka kulle jaka ko akwatin da ba zaka rike a hannunka ba. Dalili shine jami'an tsaro zasu nemi bincike su tabbatar da abubuwan dake ciki domin kariyar dukkan fasinjoji. Idan ka kulle, to ana iya balle kwadon.

2. Idan kana dauke da Kwamputa ta hannu, to ka cire ta daga cikin jakarta idan ka doshi wurin da ake shigewa ta gaban jami'an tsaro masu bincike, ka saka ta dabam da jakarta a kan na'urar bincike.

3. Idan akwai sakonni ko kayayyakin da kake son bayarwa kyauta ga wasu, kada ka nade cikin takarda ko laida, domin watakila jami'an tsaro masu bincike zasu so su ga abinda ke cikin kayan.

4. Idan an zo jera kaya cikin akwati ko jaka, a yi hattara kada a shake akwati ta yadda ba zai rufu da sauki ba, domin idan aka zo aka sake budewa a filin jirgi domin bincike, wadanda suka bude zasu fuskanci wahalar rufewa. Idan kana dauke da fim na daukar hoto, ka rike shi cikin jakar dake hannunka. Kayayyaki kamar kamfai, reza da abin aski, man shafawa, da na goge baki da makamantansu, sai a sanya a cikin farar laida ta yadda za a iya ganin abinda ke cikin laidar ba tare da an bude ko an taba su da hannu ba.

5. A guji rikewa ko sanya wani abu mai karfe a jiki, domin wannan zai sa na'urar sunsuno karfe ta yi kara, ya janyo wa mutum jinkiri sosai.

6. A isa filin jirgin sama da wuri domin tabbatar da cewa an kammala komai cikin tsanaki. Ka tabbatar da cewa ka tuntubi kamfanin jirgin samanka kafin ka bar gida.

7. Domin samun cikakken bayani game da harkokin tsaro a filayen jiragen sama na Amurka, zaka iya bude wannan dandali na hukumar tsaro a duniyar gizo, inda zaka iya ganin bayani kan abubuwan ad zaka iya shiga da su cikin jirgi da wadanda ba zaka iya ba. Ga dandalin nan: www.TSATavelTips.us

8. Ga kuma wasu wuraren da za a iya dubawa domin samun cikakken bayani, a cikin harshen Turanci, kan batutuwan ad suka shafi kawo ziyara nan Amurka, kamar abubuwan da mutum zai bukata na takardu da sauransu.

Wasu Takardu Mutum Yake Bukata Domin Shiga Amurka?

Yaya Ake Samun Takardar Biza Ta Zuwa Amurka?

Kula da Lafiyar Matafiyi - Daga Cibiyar Kare Cututtuka ta Amurka

Shawarwari Ga Matafiyi Ta Jirgin Sama

Bayanai Game Da Tsaro A Filayen Jirgin Sama

Sassauci Ga Nakasassu, da Yara da Masu Sanye Da Tufafin Da Addininsu Ya Bukata

Zafi Ko Sanyi Zaka Taras A Inda Zaka A Amurka? Duba Ka Gani

Bayani Game Da Jihohin Amurka. Idan Ka Bude Sai ka Zabi Jihar Da Kake Son bayaninta

Bayanan Muryar Amurka Game Da Biranen Amurka

Wuraren Shakatawa

Gandun Shakatawa A Amurka

XS
SM
MD
LG