Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tana Bukatar Agajin Gaggawa... - 2003-07-30


Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta ce ana bukatar agajin abinci na gaggawa domin mutane fiye da miliyan daya da rabi wadand ake fuskantar ukubar yunwa a sanadin yakin basasa da fari a kasar Uganda.

Hukumar tana neman agajin dala miliyan 54, tana mai kashedin cewa muddin ba gudumawa aka samu cikin gaggawa ba, to abincin da take da shi zai kare nan da watan satumba.

Hukumar ta ce musamman ta damu da cutar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin mutanen dake zaune cikin sansanonin wucin gadi, inda fararen hula suka nemi mafaka daga hare-haren 'yan tawayen arewacin Uganda.

wata mai magana da yawun hukumar ta ce rashin tsaro ya gurgunta ayyukan rarraba kayan agaji da kuma harkokin noma a kasar.

Har ila yau, hukumar ta ce mutane dubu 655 suna bukatar agaji a sanadin fari a yankin Karamoja na arewa maso gabashin Uganda.

XS
SM
MD
LG