Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Saman Yakin Isra'ila Sun Kai Hari Kan Hezbollah A Lebanon - 2003-08-11


Jiragen saman yakin Isra'ila sun yi luguden wuta a kan sansanonin Hezbollah a kudancin Lebanon, a bayan da kungiyar ta 'yan sari-ka-noke ta bude wuta da bindigogin igwa daga tsallaken iyaka ta kashe wani saurayi dan Isra'ila ta raunata wasu hudu.

Babu wani rahoton da aka samu ya zuwa yanzu na jikkata daga wadannan hare-haren jiragen yakin da Isra'ila ta kai. Isra'ila ta kai wannan harin a bayan da ta ce Hezbollah ta cilla albarusan ragargaza tankokin yaki wadanda suka kashe wani saurayi mai shekaru 16 da haihuwa.

Hezbollah ta ce ta harba makaman kabo jiragen sama a kan jiragen yakin Isra'ila da suka shiga yankin samaniyar Lebanon.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, yayi tur da farmakin na jiya lahadi.

Wannan lamari ya biyo bayan musanyar wutar da aka yi da bindigogin igwa a ranar Jumma'a a tsakanin Isra'ila da dakarun Hezbollah a yankin gonakin Shebaa na bakin iyaka da ake rikicinsu.

XS
SM
MD
LG