An yi jana'izar tsohon shugaban kasar Uganda, Idi Amin Dada, wanda ake dorawa laifin mutuwar dubban mutane, a kasar Sa'udiyya, inda ya rasu jiya asabar.
Malam Idi Amin yayi makonni da dama yana fama da rashin lafiya mai tsanani a wani asibiti a Jeddah. An binne shi jim kadan a bayan rasuwarsa jiya asabar da safe. An ce Idi Amin ya rasu yana da shekaru 80 da haihuwa, amma wasu rahotanni sun ce shekarunsa 78 ne.
An ce ya nuna tsananin mugunta da keta hakkin jama'a a tsawon mulkinsa na shekaru 8 daga 1971 zuwas 1979. A karkashin mulkin nasa, an kashe mutane masu yawan da har aka kasa tona kaburbururan da za a binne su, saboda haka aka yi ta jefa gawarwakinsu a cikin kogin Nilu.
A shekarar 1972, Idi Amin Dada, ya kori duban Asiyawa wadanda suka mallaki akasarin kamfanonin kasar da kanianaye harkokin kasuwanci a wannan kasa, yana mai fadin cewa Ubangiji ne Ya fada masa yayi hakan a mafarki. Wannan matakin ya jefa tattalin arzikin Uganda cikin mummunar matsala.
Idi Amin Dada ya nada kansa shugaban Uganda na tsawon rai, amma daga baya an kore shi daga kasar tasa. Ya gudu zuwa Libya, daga nan ya koma Iraqi kafin ya koma kasar Sa'udiyya inda aka kyale shi ya zauna, muddin dai ba zai gudanar da harkokin siyasa ba.
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya fadawa iyalan Idi Amin cewar suna iya kai gawarsa su binne a Uganda, amma kuma gwamnati ba zata dauki dawainiyar jana'izar, ko kuma karrama shi ba.
Wasu al'ummar Uganda dai sun bayyana farin cikin mutuwar mutumin da a ganinsu mai mulkin kama karya ne, yayin da wasu suke bakin cikin shugaban da suke gani a zaman zakaran bakar fata a kan turawa.