Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Tsara Wani Kudurin Da Zai Nemi Wakilan MDD Su Taimaka A Iraqi - 2003-08-22


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce Amurka tana aiki kan wani sabon kudurin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, wanda zai karfafa guiwar wakilan majalisar da su tallafawa rundunar taron dangin da Amurka take yi wa jagoranci a Iraqi.

A lokacin da yake magana a birnin New York, Mr. Powell ya ce nan ba da jimawa ba jami'an jakadancin Amurka za su fara tattaunawa da kasashen dake da wakilci a majalisar kan irin lafazin da wannan kuduri zai kunsa.

Har ila yau a jiya alhamisr, Mr. Powell ya ce yayi farin ciki da ya ji babban sakataren MDD, Kofi Annan, yana fadin cewa majalisar zata ci gaba da gudanar da ayyukanta a Iraqi, duk da harin bam na kunar-bakin-wake da aka kai kan hedkwatarta ta Bagadaza a ranar talata.

Mr. Annan ya ce MDD ba ta da wani shiri na tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Iraqi.

Ya ce duk wani karin aikin da majalisar zata iya takala a Iraqi zai mayar da hankali ne kacokam kan sake gina tattalin arziki da cibiyoyin siyasar kasar.

XS
SM
MD
LG