Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colin Powell Yana Shirin Sauka A Iraqi - 2003-09-14


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, yana shirin ganewa idanunsa halin da ake ciki a Iraqi, a bayan da ya tattauna makomar kasar da sauran kasashe masu ikon hawa kujerar-na-ki a MDD.

A yau lahadi Mr. Powell zai isa kasar Kuwaiti, inda zai gana da shugabanni kafin ya tashi zuwa Iraqi.

Jiya asabar a birnin Geneva, Mr. Powell da takwaran aikinsa na kasar Faransa sun bayyana ra'ayoyin da suka saba sosai da juna kan lokacin da ya kamata a mayar da mulki hannun 'yan Iraqi.

Ministan harkokin wajen Faransa, Dominique de Villepin, ya bukaci da a mayar da mulkin nan da ranar 31 ga watan Oktoba. Ita ma kasar Rasha tana son a gaggauta mayar da mulki hannun 'yan Iraqi. China ta ce MDD ce ya kamata ta yanke wannan shawara. Britaniya ta bayyana muhawarar da aka yi a zaman mai ma'ana.

Mr. Powell ya ce mayar da mulki cikin gaggawa zai sa duk gwamnatin da za a kafa ta wargaje cikin kankanin lokaci.

A lokacin da yake Iraqi, Mr. powell zai gana da majalisar Mulkin kasar mai wakilai 25 da kuma hukumomin Amurka masu gudanar da mulkin kasar.

Jiya asabar a Fallujah kuma, mutanen wannan gari dake fusace sun yi ta harbi a sama a lokacin da ake jana'izar wasu 'yan sanda takwas wadanda sojojin Amurka suka kashe bisa kuskure ranar Jumma'a. Akwai wani mai gadi dan kasar Jordan a cikin wadanda aka kashe din.

XS
SM
MD
LG