Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Bai San Ko Za A Iya Gano Wanda Ya Fallasa 'Yar Leken Asiri Ba - 2003-10-08


Wa'adin da fadar White House ta tsayar na mika duk wani bayanin dake da nasaba da fallasa sunan wata 'yar leken asiri ya wuce, a bayan da shugaba Bush ya ce ofishin nasa yana bayar da cikakken hadin kai ga masu binciken wannan al'amari.

Fadar White House ta umurci ma'aikatanta da su mika dukkan bayanan da aka dauka a na'urori, da jerin lambobin wayar da suka buga ko aka bugo musu da kuma bayanan da suka rubuta na yau da kullum ya zuwa daren jiya talata.

Ma'aikatar shari'a ta tarayya tana binciken zargin cewa wani jami'in gwamnatin shugaba Bush ya nemo 'yan jarida ya fallasa musu sunan wata jami'ar leken asiri, a wani matakin daukar fansar siyasa a bayan da mijinta ya soki manufofin Iraqi na shugaba Bush.

A jiya talata, shugaba Bush ya ce bai san ko jami'an bincike na tarayya za su iya gano mutumin da ya fallasa sunan wannan mace mai aikin leken asiri a boye ba.

XS
SM
MD
LG