Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Iran Ba Ta Yarda Ta Daina Tace Karfen Uranium Ba - 2003-10-17


Shugaban hukumar kula da makamshin nukiliya ta MDD, ya ce har yanzu Iran ba ta yarda ta daina tace karfen Uranium wanda za a iya yin amfani da shi wajen hada makaman nukiliya ba.

Amma kuma an ambaci Mohammed el-Baradei yana fadin cewa Iran ta yarda zata amsa koke-koken da hukumar ta gabatar mata a game da shirin nukiliya na Iran din.

Shugaban hukumar yayi wannan furuci a bayan da ya tattauna da jami'an Iran jiya alhamis a birnin Teheran.

Jakadan Iran a Hukumar Makamshin Nukiliya ta MDD, Ali Akbar Salehi, yayi alkawarin cewa za a samu gagarumin ci gaba nan ba da dadewa ba. Hukumar ta bai wa Iran wa'adin nan da ranar 31 ga watan nan na Oktoba kan ta gabatar da shaidar cewa ba ta kera makaman nukiliya.

Iran ta ce shirinta na nukiliya na samar da wutar lantarki ne kawai.

XS
SM
MD
LG