An kashe sojan Amurka daya da wasu fararen hula biyu 'yan Iraqi a gwabzawa ta baya-bayan nan tsakanin sojojin Amurka da 'yan Iraqi a garin Fallujah.
Rundunar sojan Amurka ta ce an kai hari kan sojojin Amurka da nakiya, aka kuma bude musu wuta da kananan bindigogi a lokacin da suke yin sintiri a wannan gari dake yamma da birnin Bagadaza.
Sojojin sun mayar da wuta, inda shaidu suka ce an rutsa da fararen hula biyu a tsakani.
Wannan tashin hankali na baya-bayan nan ya zo a daidai lokacin da wata sananniyar kungiyar kare hakkin bil Adama ta zargi rundunar sojojin Amurka da laifin kasa gudanar da bincike sosai dangane da mace-macen fararen hula.
Kungiyar "Human Rights Watch" ta ce ta tabbatar da mutuwar fararen hula 20 'yan Iraqi a hannun sojojin Amurka a birnin Bagadaza, daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa karshen watan Satumba.