Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashi 50 Cikin 100 Na Al'ummar Turai Sun Yi Imanin Cewa Isra'ila Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya A Duniya - 2003-11-03


Shugabannin yahudawa da na Isra'ila sun yi tur da wata kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a ta Tarayyar Turai wadda ta ce kashi 60 daga cikin 100 na turawa sun yi imanin cewa Isra'ila ce babbar barazana ga zaman lafiya a duniya.

Shugaban wata kungiyar dake yakar nuna kin jinin yahudawa a duniya ya ce wannan kuri'ar raba-gardama bangare ce ta "kyamfe din bakanta" Isra'ila da magoya bayanta.

Marvin Hier na Cibiyar Simon Wiesenthal dake nan Amurka ya ce kuri'ar ta nuna cewa Tarayyar Turai ba zata iya taka wata rawa a shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya nan gaba ba.

Ministan kula da yahudawan dake kasashen ketare a gwamnatin Isra'ila, Natan Sharansky, ya shaidawa kafofin yada labarai na Isra'ila cewa kuri'ar ta gaskata ikirarin cewa kin jinin yahudawa ne ke rura wutar sukar Isra'ila.

Wannan kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a da Majalisar Zartaswar Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci a gudanar, ta nuna cewa kusan kashi 60 daga cikin 100 na al'ummar nahiyar Turai sun yi imanin cewa Isra'ila ta fi barazana ga zaman lafiya a duniya fiye da kasashen Koriya ta Arewa, Iran ko Afghanistan.

An buga wasu daga cikin abubuwan da kuri'ar neman ra'ayoyin jama'ar ta gano a ranar Jumma'a cikin jaridar "International Herald Tribune" kafin Majalisar Zartaswar tarayyar Turai ta fito da cikakken sakamakon a yau litinin.

XS
SM
MD
LG