Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Tawagar MDD Ta Doshi Afirka Domin Binciken Keta Takunkumin Makamai A Somaliya - 2003-11-12


Wata tawagar Kwamitin Sulhun MDD ta doshi Afirka domin nazarin keta takunkumin makaman da aka sanyawa Somaliya, wanda kuma yana iya yin barazana ga yankin baki daya.

Wannan tawaga ta kwararru a fagen makamai, karkashin jagorancin jakadan kasar Bulgariya, Stefan Tafrov, zata ziyarci kasashen Afirka 6 domin tattauna batun kafin ta gana da shugabannin Somaliya a kasar Kenya.

Wannan ziyara ta zo kwanaki kadan a bayan da aka wallafa wani rahoto na MDD wanda ya ce an yi amfani da Somaliya a zaman sansani wajen kitsa mummunan harin bam da 'yan al-Qa'ida suka kai kan wani hotel na kasar Kenya a shekarar da ta shige.

Rahoton ya ce keta takunkumin makaman a kai a kai yana nufin cewa 'yan ta'adda za su iya shigarwa tare da fitar da makamai daga cikin kasar ta Somaliya.

XS
SM
MD
LG