Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dick Cheney ya amince da zaben Jam'iyar Republican don sake tsayawa takara - 2004-09-02


Mataimakin kasa Dick Cheney ya amince da zaben Jam'iyar Republican don sake tsayawa takara. Mr Cheney ya bayana zaben shugaban kasa na wannan shekarar ta 2004 a zaman mai mahimmanci a tarihin kasar ta Amurka. Ya yabawa kokarin Mr Bush na yaki da ta'addanci, yayin da ya kuma ya yi kakkausar suka ga dantakarar Damokarat, John Kerry.

Mr cheney ya sheda wa wakilai a wajen babban taron cewa zaben na wannan shekara na da matukar mahimmanci a tarihin kasar. Akan rawar da Amurka zata taka a duniya, Mr Cheney ya ce akwai babbanci sosai a tsakanin shugaba Bush da kuma shi John Kerry.

Mataimakin shugaban kasar ya zargi dantakarar damokarat da yawan sauya ra'ayin sa akan mahimman batutuwa. Yace " akan batun Iraqi, John Kerry bai yarda da 'yanjam'iyar sa da dama ba. sai dai kuma babbar rashin aminta itace shi kansa bai yarda da kansa ba." Yace kom-gaba kom-bayan da ya cika yi ya nuna irin halin sa na kasa daukar matsayi, wanda hakan wani sako ne na rudani." Ya kuma ce John Kerry biyu ne Amurkawa ke gani.

Mr Cheney ya ambato ababe mahimmai da ya ce manayan nasarori ne da gwamnatin shugaba Bush ta samu a cikin shekaru ukku da rabi da tayi ta na mulki. Akan batutuwa na cikin gida, ya ambato sauye-sauye a fannin ilmi da bunkasar tattalin arziki da rage haraji a matsayin nasarorin da aka samu.

Yace "shugaban kasar mu ya fahimci siddabarun wannan babbar kasa. Ya san irin burin jama'a, yana kuma da kyakkyawar fatar alhirin da ta zama dabi'ar mutan kasar." Yace a kullum ya wayi gari, ya kan tashi da karkarfar anniyar samar da walwala da kwanciyar hankali awannan babbar kasar domin al-ummar mu masu zuwa zasu san irin 'yanci da damar da muke da ita da dai sauran. A wani abun da ba kasafe ake yi ba, wani dan jam'iyar adawa ta Damokarat ya yi wani jawabin bude babban taron Jam'iyar republican din. Shekaru goma sha biyu da suka shude, damajalisar dattawa Zell Miller ya gabatar da jawabi a wajen babban taron da aka tsayar da shugaba Bill Cliton dantakarar Jam'iyar Damokarat. Amma a wannan shekarar, yace shi kam ya kosa da abun da ya kira sanyin halin Jam'iyar damokarat din, don haka ya yanke shawarar ya ba dantakarar Jam'iyar Republican goyon baya.

XS
SM
MD
LG