Shugaba Bush na kamfen a mahimmiyar jihar West Virginia a dai-dai lokacin da binciken ra'ayin jama'a guda biyu suka nuna cewa ya dara abokin hamayyarsa John Kerry.Wannan itace lahadi biyu a jere shugaba Bush yana kamfen a West Virginia, jihar da ya lashe zabanta shekaru hudu da suka wuce kuma wurin da 'yan republican suka yi imani senata Kerry zai bukaci lashewa kafin ya ci zaben shugaban kasa.
Da alama kamfen din shugaba Bush na kara karfi a wannan jiha domin tabbatar da karfinsu wanda ya jawo suka ziyarci jihar har sau takwas kuma da alama basu gama ziyarar ba. 'Abin alfahari ne dana sake dawowa West Virginia', inji Bush, kamar ya zama al'ada inzo nan. 'Ya kamata mutanen jihar nan su fahimci cewa ina so in sake samun nasara a wannan jihar.'
Wannan yana nufin samun 'yan democrat su jefa kuri'unsu ga jami'yyar republican a watan Nuwamba. A makarantar sakandare ta Parkersburg, shugaba Bush yayi maraba da wasu 'yan democrat a taron da aka yi a filin wasan makarantar. 'Ina so in gode muku saboda zuwanku. Sakona na kowa da kowa ne. Ya kara da cewa,' Amintacciyar kasa mai karfi da bunkasa ga duk dan kasa.'
'Yan jihar West Virginia sun saurari sakon shugaban, wato tattalin arziki yana kara inganta shi kuwa Senator kerry yana son ya kara haraji sannan kuma shi(Bush) ne ya kamata ya ci gaba da mulki saboda tunkarar kalubalen ta'addanci dake fuskantar kasar.'Nayi imani babban aikin shugaba shine ya kare Amurkawa', inji Bush. 'Idan Amurka ta nuna gazawa a wannan karnin to duniya zata shiga wani hali na hatsari. Wannan baya abkuwa a karkashina. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a har guda biyu a jaridun Time da Newsweek sun nuna cewa shugaba Bush yana sama da senata Kerry da ratar sama da kashi goma. Idan har wannan rata ta ci gaba to ba shakka Bush zai zama ya fito da karfi a karshen babban taron republican fiye da yadda senata Kerry ya fito daga taron 'yan democrat a watan Yuli. Manajan kamfe na Bush, Ken Mehlman yace duk da cewa kuri'ar jin ra'ayin na kara musu kwarin gwiwa anyi azarbabi ace shugaban na kan gaba bayan watanni ana kunnen doki.
'Ina zaton cewa zaben zai kasance sai an gwabza sosai a kowane lokaci' inji Mr. Mehlman. Amma idan muka samu sakamako mai kyau a mako mai zuwa to zamu samu sanin halin da ake ciki ta bangaren rata. Shugaba Bush ya ci gaba da yawon kamfen dinsa bayan gama babbban taron jam'iyyarsa tare da zagaye cikin mota zuwa wata mahimmiyyar jiha ta Missouri a ranar litinin da talata.