Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ran Arafat na hannun Allah in ji jakadiyar Palasdinawa - 2004-11-10


Wata jami’ar Palasdinawa ta sake cewa ba za’a cire injin da yake taimakawa Yasser Arafat ke rayuwa ba a asibitin da yake a Paris amma a hirarta da gidan rediyon Faransa ta ce wani babban malami ya isa Paris don zama kusa da Yasser Aarafat ko da ta kasance ya rasu. Jakadiyar Palasdinu a Faransa, Leila Shahid ta bayyana cewa rayuwar Arafat tana hannun Allah. Madam Shahid ta musanta labarin cewa tuni Arafat ya rasu ta ce likitocin Faransa na iya kokarinsu don ceto ran Arafat. ‘Dole mu tsaya mu ga abinda Allah ya kaddara masa.'

Madam Shahid ta kuma ce wani babban malamin Islama, Sheikh Tammim ya isa Paris don zama a kusa da Arafat kamar yadda yahudawa da kiristoci ke kiran malamansu kusa da mai alarmar mutuwa. Wannan kalamai na Madam Shahid sune na karshe na karyata mutuwar Arafat daga bakin wani shugaban Palasdinawa. Wasu rahotanni sun ruwaito likitocin Faransa suna cewa an samu gudanar jini a cikin kwakwalwar Arafat wanda alama ce ta cewa yana iya mutuwa a cikin awowi.

An kuma samu bayanan cewa shugabannin Palasdinawa suna shirye-shiryen jana’izar Malam Arafat a Alkahira a inda kuma za’a binne shi a birnin Ramallah da ke yamma da bakin kogi bayan samun amincewar hukumomin Isra’ila

XS
SM
MD
LG