Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta tabbatar da cewar ta jingine kokarin da take na inganta nagartar sinadarin uranium - 2004-11-15


Kasar Iran zata dakatar da kokarin da ta ke na inganta nagartar sinadarin uranium daga ranar 22 ga wannan watan na Nuwamba. Hakan zai faru ne a matsayin daya daga cikin sharuddan yarjejeniyar da kasar ta cimma da kasashen Turai, da naufin sassauta ire-iren damuwar dake akwai game da shirin da kasar ta ke yi game da nukiliya.

A cikin wata gajeriyar tattaunawa da manema labarai a yau litinin, wani mai magana da yawum ma’aikar harkokin wajen Iran Hamid Reza Asefi ya ce wannan mataki da kasarsa ta dauka, alama dake nuna cewa Iran din da gaske take. Amma kuma yace dakatawar da kasar tasa tayi game da inganta nagartar uranium, ba wai ta illa-ma-sha-Allahu ba ce. Ba’a dai bada cikakakken bayanin ita wannan yarjeniyar da aka sanar da ita a jiya Lahadi ba.

Kasahen Turai dai sun gargadi gwamnatin Iran cewa zasu goyi bayan a mika al’amarinta zuwa gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin yiyuwar sanya mata takunkumi, idan dai har bata bar shirinta na inganta sinadarin uranium ba.

Shi dai irin wannan shiri na kokarin inganta sinadarin uranium ana iya amfani da shi wajen kera makaman kare-dangi na nukiliya. Sai dai ita Iran ta dage cewar tana wannan shiri ne domin samar da wutar lantarki kurum. Ita kuma Amurka na zargin ta da cewar shirin nata na kokarin samar da makaman nukiliya ne, amma cikin sirri.

XS
SM
MD
LG