Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ba za ta amince da sakamakon zaben Ukraine ba, in ji Powell - 2004-11-26


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell ya ce Amurka ba za ta amince da sakamakon zaben Ukraine ba saboda an tafka magudi. Amma ya shaidawa ‘yan jaridu a ranar laraba cewa ba a makara ba wajen yin gyara kan rikicin zaben da ya shafi al’umar Ukraine. Mista Powell ya jaddada kashedin Amurka na cewa za a samu matsala a dangantaka tsakanin Amurka da Ukraine muddin hukumomi a Kiev ba su hanzarta yin gyaran da ya kamata ba dangane da sakamakon zaben.

A lokacin da ya bayyana don yiwa ‘yan jaridu bayanin rana-rana, Mista Powell ya ce har yanzu akwai sauran lokaci wajen shawo kan wannan rikici. Ya kuma ce Amurka a yanzu ta damu da ganin an shawo kan rikicin siyasar ne ta lumana ba ta daukan mataki kan kasar ba.’’ A yanzu muna duba hanyar da za a samu ci gaba a rikicin amma ba daukar mataki a kan batun ba don samun mafita wadda za ta nuna irin miradin mutanen Ukraine a zabe mai cike da gaskiya da ‘yanci don samun amincewar ‘yan kasar da kuma kasashen duniya’’, in ji Mista Powell.

Mista Powell ya ce ya yi magana da shugaban Ukraine, Leonid Kuchma a inda ya ja kunnensa kan yin amfani da karfi kan masu zanga-zanga kan zaben ya kuma nemi da ayi amfani da wannan lokaci don samun damar sasanta rikicin zaben tsakanin ‘yan takarar shugaban kasar guda biyu.

Sakataren ya kuma ce sun yi magana mai mahimmanci kan wannan matsala da ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov wadda gwamnatinsa tuni ta nuna goyon bayanta ga wanda aka ce ya lashe zaben, firaminista Victor Yanukovich. ‘’ A yanzu abinda dukkaninmu muka damu da shi shine samun mafita ta hanyar doka da dokokin Sharia dan sasanta zargin magudin zabe da senata Richard Lugar da sauran masu sa ido suka yi. Kuma mu a yanzu muna bin hanyar diflomasiyya ne da manufofin siyasa don shawo kan wannan rikicin. Ba wai muna yin jayayya da Rasha ba ne kan wannan rikici, muna so ne muga an mutunta ‘yancin zaben mutanen Ukraine.’’

Jami’an gwamnatin Amurka sun yi zargin cewa a lokacin zaben Ukraine an karkata dukiyar gwamnati wajen taimakawa kamfen din Mista Yanukovich da kuma cewa an yi amfani da kafofin watsa labaran gwamnati wajen bata dan takara mai goyon bayan kasashen yamma, Victor Yushchenko. A lokacin tataunawar ta su da ‘yan jaridu , Mista Powell ya ce babu wani mataki da aka yanke kan yadda za a shawo kan rikicin amma ya ce akwai shawarar a sake yin zaben sannan kuma akwai wasu hanyoyi da za a iya yin nazarinsu. Ya kuma ce har idan Ukraine ta bi hanyar da ta dace za ta samu taimako daga Amurka da tarayyar turai da kuma Poland wadda shugabanta, Alexandr Kwasneiwski ya amince ya sasanta rikicin.

XS
SM
MD
LG