Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An bude taron shugabannin kasashen kudu-maso-gabashin Asiya - 2004-11-29


Shugabannin gwamnatocin kungiyar kasashen kudu-maso-gabashin Asiya sun fara taron kwana biyu a Laos da burin samar da hadaddiyar kungiyar tattalin arziki ta yankin Asiya cikin shekaru shida masu zuwa. Tana da kuma burin fadada yarjejeniya kan yankin cinikayya na bai daya da sauran kasashe masu karfin tattalin arziki na yankin Asiya. Firaministan Laos, Boungnag Vorachit ne ya bude taron a inda ya ce sababbin kalubale kamar ta'addanci da karuwar farashin danyan man fetur da yaduwar cututtuka cikin sauri ya sanya dole a kara samun hadin kai tsakanin mambobin kungiyar na kasashe goma.

Ya kuma ce dangantaka tsakanin kungiyar da sauran kasashen Asiya za ta kara inganta. Mai magana da yawun gwamnatin Laos, Yong Chantalangsy ya yi bayanin cewa shugabannin kungiyar sun amince da yin shirye-shiryen taronsu na shekara-shekara tare da kasar Sin da Japan da kuma Koriya ta kudu. 'Shugabannin sun yadda su yi taron kasashen gabashin Asiya tare da na kungiyar kasashen kudu-maso gabashin Asiya na goma sha daya a Kuala Lumpur a shekara mai zuwa,' in ji shi.

Wasu suna ganin wannan taron a matsayin matakin farko a kokarin samar da kuniyar gamayyar tattalin arziki ta gabashin Asiya wadda za ta game kusan kashi daya cikin ukun harkokin tattalin arzikin duniya. Shugabannin kungiyar sun kuma yi alkawarin daukar nauyin gudanar da taronsu na farko da kasar Rasha a shekara mai zuwa. Ana sa ran ministan harkokin wajen Rasha zai sanya hannu a kan yarjejeniyar dangantaka da kungiyar a taron da ake yi na wannan makon.

Kungiyar ta kuma sanya hannu a kan yarjejeniya da Sin kan samar da 'yankin kasuwanci na bai daya mafi girma a duniya. Haka kuma akwai tattaunawa kan samar da wani 'yankin kasuwanci na bai daya tare da Koriya ta kudu da Japan da kuma Indiya , akwai kuma irin wannan shiri da Australia da New Zealand. Mai magana da yawun kungiyar, Jun Abad ya lura cewa sakamakon wannan kungiya, kudin fito kan yawancin kayayyaki sun ragu da kashi biyar. Ya kuma ce kasashe shida masu karfin tattalin arziki na Brunei da Indonesia da Malaysia da Singapore da Thailanda da Philppines a ranar litinin sun amince da kawar da kudin fito a bangarori masu mahimmanci guda goma sha daya. Bangarorin sun hada da motoci da harkokin dazuzzuka da kayan masaku da kayan da ake sarrafawa wanda su ne sama da rabin abinda ake ma'amala da su a yankin. Karkashin wannan shirin, kasashe shida na wannan kungiya za su kara kaimi wajen kawar da duk wani kudin fito i zuwa shekara ta dubu biyu da bakwai, in ji Mista Abad.

Sauran kasashe hudu na kungiyar Bama da Kambodiya da Laos da Vietnam su ma za su bi sahu a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu. Shugabannin sun amince da su samar da wani asusun raya kasa don taimakawa kasashe marasa karfi don cinma burin samar da kasuwar bai daya. Kungiyar ta kuma amince da kara hadin kai a harkar tsaro da al'adu don mayar da kungiyar gamayyar yanki a shekara ta dubu biyu da goma. Manyan 'yan kasuwan yankin bayan wani taro sun gayawa shugabannin cewa samar da yankin kasuwanci na bai daya na da mahimmanci amma kuma a bawa harkar ingnta hanyoyi da samar da sufuri da sa ka'idojin shigar da kaya da kuma saka jari mahimmanci.

XS
SM
MD
LG