Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Australia na son tsattsauran matakai kan yaduwar makamai - 2004-11-30


Ministan tsaron kasar Australia, Robert Hill ya yi kira da kasashen yankin Asiya da Pacific da su kara mayar da hankali wajen hana yaduwar makamai masu hatsari. Wannan kira na Senata Hill ya zo ne a lokacin bude taro kan hana yaduwar makamai a Sydney. Ministan , ya ce yankin Asiya da Pacific wanda ke da manyan tashoshin ruwa da tashoshin jiragen sama a duniya dole ya kara sa ido kan hana fataucin makamai masu hatsari. Senata Hill ya yi bayanin a lokacin da wakilai daga kasashe goma sha tara suka taru a Sydney don tattauna abubuwan da suka shafi dokoki da kayan aiki da bayanan sirri masu dangantaka da fataucin makamai. Gwamnatin Amurka ce ta kirkiro wannan kokari na hana fataucin makamai ba bisa ka’ida ba .

Senata Hill ya ce akwai aiki mai yawa domin a yanzu matakan hana yaduwar makamai masu hatsari ba su isa su hana fadawar makaman hannaun ‘yan ta’adda ba . Jami’in tsaron ya kuma ce gwamnatin Canberra ta yi kashedi ga kamfanonin Australia kan su sa ido kan musayar fasaha wadda za a iya amfani da ita wajen kera irin wadannan makaman.’’Akwai bayanai masu cewa wasu kamfanonin sun bayar da irin wannan fasaha cikin rashin sani wadanda aka yi amfani dasu a harkar makamai masu hatsari’’, in ji Mista Hill.’’ Musamman abinda ya shafi ayyukan bincike wanda abu ne da mu ke sa ido sosai.’’. Sojojin ruwan Australia da jami’an hana fasakaurinsu da na Amurka sun shiga wani shirin atisaye a Japan a watan da ya wuce. Jami’an sun yi atisayenne kan yadda za su gano su kuma kama jirage masu dauke da makaman kare-dangi da masu guba da dai sauran abubuwan da ake hada su. Masu goyon bayan wannan shirin tsaro na hana yaduwar makamai sun ce atisayen ba an yi shi ne don matsawa wata kasa ba. To amma ba haka Koriya ta Arewa ke kallon abin ba.

Ta kira wannan atisaye na yankin Japan a matsayin tsokana. Australia ta ce kokarin Pyongyang na mallakar makaman kare dangi babbar barazanar harkar tsaro ce a yankin Asiya da Pacific. Koriya ta Arewa ta yi ikirarin cewa tana gina tashar makamin kare-dangi abinda ya saba alkawarinta na tabbatar da hana yaduwar makaman kare-dangi a yankin. Amurka na zargin cewa Koriya ta Arewa ta mallaki bama-baman nikuliya guda biyu.

XS
SM
MD
LG