Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar Iran sun kai dari hudu - 2005-02-23


Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a kudu maso gabashin kasar Farisa bayan abkuwar wata girgizar kasa a safiyar Talata wadda ta halaka sama da mutane dari hudu. Wadanda suka tsira ammma suka galabaita na fama da tsananin sanyi da kuma fargabar abinda ya faru. Da dama daga cikin wadanda suka tsira na korafin rashin mahalli.

Duk da korafin rashin isasshen abinci da kuma mahalli a bangaren wadanda suka tsira daga wannan bala’in girgizar kasa mai karfin gaske gwamnatin Iran ta ci gaba da dagewa kan kin karbar duk wani taimakon agaji daga kasashen waje. Girgizar kasar ta lalata kauyuka da dama wasu ma gaba daya kauyukanne suka lalace wasu kuma wasu sassansu ne kawai barnar ta shafa.

Ita dai wannan girgizar kasar ta kai mizanin shida da digo hudu a ma’aunin Ritcher kuma ta abku ne a wani wuri mara nisa daga inda aka samu irin wannan girgizar kasa wadda ta abku a watan Disamban shekara ta dubu biyu da uku wadda ta halaka mutane dubu talatin. Jami’an Iran sun bayar da kiyasin cewa kimanin mutane dubu talatin ne wannan girgizar kasa ta shafa. A safiyar Laraba ne kuma aka ce jami’an sojan Iran suka zakulo wasu ‘yan mata guda biyu da ransu daga cikin kurakuzan gine-gine a wani kauyen da ke kan wani tudu.

Ruwan sama mai hade da kankara na kawo cikas ga aikin ceton abinda kuma ke kara wahalhalu ga wadanda suka tsira daga wannan bala’in girgizar kasa. Mutanen da suka tsira daga wannan bala’i kan taru su zagaye wutar da suka hura don jin dimi.

XS
SM
MD
LG