Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta ce babu sauyin mataki kan Iran - 2005-03-14


Gwamnatin shugaba Bush na Amurka ta ce babu wani sauyin matsayi daga bangarenta kan shirin nukiliyar Iran sai dai kawai kokarin bin hanyar diflomasiyya daga bangaren kasashen Turai. A makon da ya wuce ne gwamnatin Bush ta bayyana kudurinta na bayar da taimakon tattalin arziki ga Iran wato Farisa don ta mayar da shirinta na mallakar nukiliya zuwa samar da makamashi kawai.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice wadda ta bayyana a shirin gidan talibijin na CBS ta ce Iran na fuskantar kalubale daga kasashe da dama. Ta kuma ce,’’ a baya mun ce muna goyon bayan shigar Turai cikin wannan batu ta hanyar diflomasiyya. Abinda shugaba Bush ya yi yanzu shine dada goyon baya ta hanyar janye kinmu ga abubuwan da Turai ta nemi da a yiwa Iran.’’ Madam Rice ta kuma ce Rasha ta amince da ta hana kokarin Iran na mallakar makaman nukiliya ta yarjejeniyar dawowa da Rashan wasu rodunan da aka yi amfani da su ga Rashan.

Shima wani babban dan jam’iyyar democrat a kwamitin harkokin kasashen waje Joe Biden da ya bayyana a gidan talibijin na CBS din ya bayyana kudurin Amurka na ganin an bayar da taimakon tattalin arziki ga Iran tare da kuma la’akari da shirin kasashen Turai na sanya mata takunkumi muddin hanyar diflomasiyya ta gaza. ‘’Anya Iraniyawa za su jingine shirinsu na mallakar makamin nukiliya? Zai yi wuya aganina. Amma idan suka ki to za mu bi sahun kasashen Turai wato daukar mataki na gaba wanda shine sanya mata takunkumi mai tsauri.’’ Ya ce. A ‘yan kwanakinnan dai jami’an Iran sun yi watsi da shirin taimakon Amurka na tattalin arziki suka kuma nuna rashin saurin tattaunawa da Turai. A Washington kuwa shugaban kwamitin harkokin kasashen wajen majalisar datttijan Amurka Senata Richard Lugar dan Republican ya nemi da a kara hakuri da Iran kasancewar a cikin wannan shekarar ne za a yi babban zaben kasar. Ya ce, ‘’ ina ga zai yi wahala ‘yan Iran su dauki wani matakin karshe a yanzu saboda suna shirin shiga zabe da kuma alama za a samu sauyin shugabanci. Nan gaba komai na iya dawowa bangarenmu. A lokacin da matasan Iran suka fara cewa suna kaunar Amurka suna bukatar cikakken ‘yanci ina ga za a iya samun abinda ake bukata.’’

Iran dai ta dage cewa shirinta na mallakar nukiliya don samar da makamashi ne saboda karuwar yawan jama’a. Amma masu kushe wannan bayani sun ce wannan alkawarin bana gaskiya bane saboda irin rashin hadin kan da kasar ke ba wa hukumar kula da hana yaduwar makamin nukuliya ta duniya.

XS
SM
MD
LG