Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim ministan kasar Lebanon mai jiran gado, kuma mai goyon bayan Sham, Omar Karami, ya sake yin murabus - 2005-04-14


Firayim ministan kasar Lebanon mai jiran gado, kuma mai goyon bayan Sham, Omar Karami, ya sake yin murabus, a bayan da ya kasa hada hancin gwamnatin da zata jagoranci kasar zuwa ga zabe a cikin watan Mayu. Mr. Karami ya ce ya kai makura, kuma ya kasa hada majalisar ministocin da zata kunshi ’yan hamayyar kasar masu adawa da Sham, ko Syria.

Ya fara yin murabus a ranar 28 ga watan Fabrairu a bayan zanga-zangar nuna kin jinin Sham, amma sai aka sake nada shi a watan Maris. Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Condoleeza Rice, ta yi marhabin da murabus din nasa a zaman wata dama ga kasar Lebanon ta gusa gaba ba tare da tsoma baki daga waje ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher, ya ce bai kamata wannan murabus ya jinkirta zaben ’yan majalisar dokoki da aka shirya yi a watan Mayu ba, ko kuma ya hana sojojin Sham janyewa daga kasar baki daya a kan lokacin da aka tsara ba. Wannan murabus na jiya laraba ya zo a daidai lokacin da ’yan kasar Lebanon suke tuna barkewar yakin basasar kasar na tsawon shekaru 15 a 1975, inda aka gudanar da bukukuwan ranar sasantawa domin murnar haɗin kan da aka samu a tsakanin Musulmi da Kiristan kasar.

XS
SM
MD
LG