Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani dattijo a cikin  manyan limaman darikar Katolika yayi kira ga sauran shugabannin darikar ... - 2005-04-18


Wani dattijo a cikin manyan limaman darikar Katolika yayi kira ga sauran shugabannin darikar su kare al’adar koyarwar katolika yayinda suke tsaida shawara kan wanda zasu zaba ya gaji marigayi pope John Poul na biyu.

Paparoma John Poul ne ya zabi Cardinal Joseph Ratzinger ya zama babban mai kare koyarwa ikilisiya. yana kuma cikin wadanda ake kyauta zaton zaɓa.Yau Cardinal Ratzinger ya jagoranci wata sujada da safe a fadar Vertican daya daga cikin ayyukan karshe kafin masu shiga zaben su fara tattaunawarsu a asirce inda zasu zabi sabon paparoma.

kardinal Ratzinger dan shekara 78 da haihuwa daga ƙasar jamus, ya shaidawa dukan shugabannin darikar da suka taru a st Peters Basilica cewa,su ki amincewa da duk wani yunkurin sauya koyarwar ikilisiyar a maisheta ta zamani nan gaba.

dukan manyan shugabannin darikar da shekarunsu suka gaza tamanin su dari da goma sha biyar sa suka hada da Cardinal Joseph Ratzinger zasu fara zamansu a kadaice ne a majami’ar Sistine inda zasu dauki rantsuwar rufe asirin taron su kuma daina hulda da duniya sai bayan an zabi sabon paparoma ya kuma amince da rike wannan mukami muddar ransa.

XS
SM
MD
LG