Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yan Liberiya sun fara yin rajista domin jefa kuri’a a zaben farko da kasar zata gudanar tun bayan yakin basasar shekaru 14. - 2005-04-26


’Yan Liberiya sun fara yin rajista domin jefa kuri’a a zaben farko da kasar zata gudanar tun bayan yakin basasar shekaru 14. Jami’ai sun fada jiya litinin cewa mutane ba su fito da yawa ba a Monrovia, babban birnin kasar, an kuma samu jinkirin fara wannan aiki a yankunan karkara da dama na wannan kasa dake Afirka ta yamma.

Masu jefa kuri’a a zaben da za a gudanar ranar 11 ga watan Oktoba zasu zabi shugaban kasa da majalisar dokokin da zasu maye gurbin gwamnatin rikon kwarya. Gwamnatin rikon kwaryar dake karkashin jagorancin Gyude Bryant, ita take jagorancin Liberiya tun bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta 2003 wadda ta kawo karshen mummunan yakin da ya lankwame rayukan dubban mutane.

Jami’an zabe sun ce suna sa ran cewa mutane miliyan 1 da rabi daga cikin mutane miliyan 4 na kasar Liberiya zasu yi rajista a cibiyoyi dubu daya da kari biyar da aka kafa a fadin kasar kafin a rufe wannan aiki na rajista a karshen watan Mayu.

XS
SM
MD
LG