Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Kungiyar Ecowas Ta Sami Kasar Niger Da Laifin Gaza Samarwa Wata 'Yar Kasar Kariya Daga Bauta


Kotun ƙolin gamayyar Afirka ta yamma ta yanke hukuncin samun Gwamnatin jumhuriyar Nijer da laifin gaza bada kariyar da ta kamata ga wata budurwar da aka tilasta mata zama baiwa.

A yau litinin kotun gamayyar ƙasshen Afirka ta Yamma dake ƙarƙashin laimar ECOWAS, ta umarci da Gwamnatin Jumhuriyar Nijer, biyan tarar Dolar Amurka dubu goma sha tara dai-dai da Saifa miliyan goma.

Alƙalain dake shari‘ar suka bada hujjar cewa Gwamnatin Nijer ta kauda kai daga gudanar da babban aikin dake kanta na kare al’ummarta da ta kauda kai taƙi kare ɗiyaucin Hadijatu Mani wadda ta kai ƙara gaban kotun tana neman hakkinta saboda saida ita baiwa da aka yi tun tana da shekaru goma sha biyu, kuma tun lokacin aka riƙa azabtar da ita ana kuma yi mata fyaɗe.

Ta kai ƙara gaban kotunne bayana da shekarunta na haihuwa suka kai 24 tare da agajin ƙungiyoyin yaƙi da bauta na Birtaniya. Idan an tuna ƙasa da ƙasa sun cimma daidaituwar hana cinikin bayai ko ina a duniya, kuma Jumhuriyar Nijer na dagacikin ƙasashen dasuka sanya hannu a kan daftarin yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG