Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Bada Sanarwar Tsagaita Wuta A Yankin Darfur


Shugaban Sudan Omar al-Bashir, ya bada sanarwa shirin tsagaita wuta kai tsaye ba tareda wani sharadi ba, a arewcin kasar na yankin Darfur da yaki ya dai-dai ta.

Shugaban yayi kira yau da akawo karshen fada tsakanin sassa dake gaba da juna,kuma a girke masu sa ido domin tabbatarda cewa duka sassan suna mutunta yarjejeniyar. Mr. Al-Bashir,yace Sudan zata bullo da shirin kwance damarar mayakan sakai,kuma ta takaita sojojinta daga amfani da makamai.

Jiya Talata wata kungiya da ake kira ta wanzarda Zaman lafiya da enci, ta bada shawarwarin samun zaman lafiya a yankin Darfur,da ya hada da shirin tsagaita wuta. Kungiyar ta kunshi ministoci da shugabanni daga Jam'iyun hamayya,kodashike 'yan tawayen yankin Darfur sun kaurace. Cikin shawarwari da kungiyar ta gabatar harda sakin fursinonin siyasa daga yankin Darfur,da kuma kirkiro mukamin mataimakin shugaban kasa domin yankin.

XS
SM
MD
LG