Wani jigon ƙungiyar al-Qaida ya gargaɗi shugaban ƙasar Amurka mai jiran gado Barak Obama da cewa shirinsa na ƙara yawan dakarun Amurka a Afghanistan ba zai cimma nasara ba.
A cikin wani saƙo da ya bayar da aka sa a shafin Duniyar Gizo na mayaƙan, mataimakin shugaban ƙungiyar ta’addancin Ayman Zawahiri ya kuma bayyana Obama a matsayin marar mutunci.
Wannan ne karo na farko da wani jigon ƙungiyar al-Qaida yake maida martani ga zaɓen Mr. Obama. Shugaban ƙasar mai jiran gado ya ce zai ƙara yawan dakarun amurka a Afghanistan domin yaƙar al-Qaida bayan abinda ya bayyana a matsayin ɗauke hankalin ƙasar da yaƙin Iraq.
Tuni
ma’aikatar tsaron Amurka ta fara shirin rage yawan dakarun ƙasar a Iraq
yayinda take ƙara ƙarfin soji a Afghanisatan inda ake samun ƙaruwar kai
hare hare.